Esta 1:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Ga abin da ya faru a zamanin Zerzes. Zerzes ya yi mulki bisan larduna 127 daga Indiya zuwa Kush. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 Ahasurus ya yi sarauta daga Hindu har zuwa Habasha, ya mallaki larduna ɗari da ashirin da bakwai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Nan da nan aka kira magatakardun fada, a ranar ashirin da uku ga watan uku, wato, watan Siban. Suka rubuta dukan umarnan Mordekai ga Yahudawa, da kuma ga shugabanni, da gwamnoni, da hakiman larduna 127 tun daga Indiya har zuwa Kush. Aka rubuta waɗannan umarnan a rubutun kowane lardi, da kuma cikin harshen kowane mutane. Aka kuma rubuta ga Yahudawa a rubutunsu da harshensu.