Daniyel 6:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Yanzu, ya sarki, sai ka yi umarni ka kuma yi shi a rubuce saboda kada a canja shi, bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Yanzu, ya sarki, sai ka tabbatar da dokar, ka sa hannu, don kada a sāke ta, gama dokar Mediya da Farisa ba a soke ta.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.”
Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.