23 “Ya sarki ka ga ɗan saƙon mai tsarkin nan, yana saukowa daga sama yana cewa, ‘A sare itacen a hallaka shi, amma a bar kututturensa daure da ƙarfe da tagulla, a bar shi can a ɗanyar ciyawar filaye, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namun jeji har shekara bakwai.’
23 Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai.
Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
Sa’an nan na ji mai tsarkin nan yana magana, wani mai tsarki kuma ya ce da wancan, “Har yaushe wannan wahayi zai tabbata, wahayi game da hadaya ta kullayaumi, da tawayen da yake kawo lalacewa, da kuma miƙa wuri mai tsarki da kuma na rundunar da za a tattake a ƙarƙashin sawu?”