Daniyel 11:24 - Sabon Rai Don Kowa 202024 Sa’ad da yankuna mafi arziki suke ji kome lafiya yake, zai kai musu hari kuma Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba abin da aka kwaso daga yaƙi, da ganima, da dukiya ga dukan mabiyansa. Zai kuma yi shiri yă kai wa mafaka hari, amma na ɗan lokaci ne kawai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki24 Ba zato ba tsammani zai kai wa lardi mafi arziki hari. Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba wa mabiyansa kwason yaƙi, da ganima, da dukiya. Zai kuma yi shiri ya kai wa kagara hari amma domin ɗan lokaci ne kawai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.