Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 9:38 - Sabon Rai Don Kowa 2020

38 Lidda yana kusa da Yoffa; saboda haka sa’ad da almajirai suka ji cewa Bitrus yana a Lidda, sai suka aiki mutum biyu wurinsa su roƙe shi cewa, “In ka yarda ka zo nan da nan!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

38 Da yake Lidda kusa da yafa take, da masu bi suka ji Bitrus na can, suka aiki mutum biyu wurinsa, su roƙe shi ya zo wurinsu ba da jinkiri ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 9:38
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A Yoffa akwai wata almajira mai suna Tabita (a harshen Girik sunanta shi ne Dokas); ita mai aikin alheri ce kullum, tana kuma taimakon matalauta.


sa’ad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawulu suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista.


Da Bitrus yake zazzaga ƙasar, sai ya je ya ziyarci tsarkakan da suke a Lidda.


Me Yarkon da Rakkon tare da sashen da yake fuskantar Yaffa.


za mu kuwa yanka dukan gumagumai daga Lebanon da kake bukata za mu kuwa yi fitonsu ta teku, su gangara zuwa Yaffa. Za ka iya kwashe su daga can ka haura zuwa Urushalima.”


Sai suka ba wa magina da kafintoci kuɗi, suka ba wa mutanen Sidon da na Taya abinci, da abin sha, da mai, don su kawo itatuwan al’ul a Yaffa daga Lebanon ta teku, yadda Sairus sarkin Farisa ya ba da umarni.


Amma Yunana ya gudu daga Ubangiji ya nufi Tarshish. Ya gangara zuwa Yaffa, inda ya sami jirgin ruwa mai shirin tashi daga tashar. Bayan ya biya kuɗin tafiya, sai ya shiga jirgi ya kama hanya zuwa Tarshish don yă tsere wa Ubangiji.


bayan ya ci abinci, sai sāke samun ƙarfi. Shawulu ya yi kwanaki masu yawa tare da almajiran da suke a Damaskus.


Wannan ya zama sananne ko’ina a Yoffa, mutane da yawa kuma suka gaskata da Ubangiji.


Bitrus ya zauna a Yoffa na ɗan lokaci tare da wani mai aikin fatu mai suna Siman.


Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus.


Ya fada musu duk abin da ya faru sa’an nan ya aike su Yoffa.


“Ina a birnin Yoffa ina addu’a, sai ga wahayi ya zo mini. Na ga ana sauko da wani abu kamar babban mayafi daga sama ta kusurwansa huɗu, ya kuma sauko inda nake.


Ya kuma gaya mana yadda wani mala’ika ya bayyana a gidansa ya ce masa, ‘Ka aika zuwa Yoffa a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ