“Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya?
A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna.
Yanzu ku daina ba’arku, in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi; Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa mini game da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar.