“Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu.
Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa, ta haka suka kasance?” In ji Ubangiji. “Wannan mutum ne nake jin daɗi, shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba, yana kuma rawar jiki ga maganata.
Ba ku sani ba? Ba ku ji ba? Ubangiji madawwamin Allah ne, Mahaliccin iyakokin duniya. Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba, kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa. “Ni ne Ubangiji, wanda ya yi dukan abubuwa, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,