Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 7:34 - Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Tabbatacce na ga wulaƙancin da ake yi wa mutanena a Masar. Na ji nishinsu na kuma sauka domin in ’yantar da su. Yanzu ka zo, zan aike ka ka koma Masar.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

34 Hakika, na ga wulakancin da ake yi wa mutanena da suke Masar, na ji nishinsu, na kuma sauko don in cece su. To, a yanzu sai ka zo in aike ka Masar.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 7:34
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;


Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.


“Ka ga wahalar kakanninmu a Masar; ka kuwa ji kukansu a Jan Teku.


sai suka gaskata. Sa’ad da suka ji cewa Ubangiji ya damu da su, ya kuma ga azabarsu, sai suka durƙusa suka yi sujada.


Allah ya ce wa Musa, “NI NE wanda NINE. Abin da za ka faɗa wa Isra’ilawa ke nan cewa, ‘NI NE, ya aiko ni wurinku.’ ”


Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum.


Na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma ’yantar da ku daga ƙasar bauta. Na aika da Musa yă jagorance ku, haka ma Haruna da Miriyam.


Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masar ta wurin annabi ya lura da shi.


Da ma za ka tsage sammai ka sauko, ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka!


Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko; ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi.


Ya aiki Musa bawansa, da Haruna, wanda ya zaɓa.


Duk sa’ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan kasance tare da mahukuncin, yă kuma cece su daga hannun abokan gāba, muddin mahukuncin yana a raye; gama Ubangiji yakan ji tausayinsu yayinda suke gunaguni ƙarƙashin waɗanda suka danne su suke kuma gasa musu azaba.


Zan sauko in yi magana da kai a can, zan kuma ɗauki Ruhun da yake kanka in mai da shi wajensu. Za su taimake ka ɗaukan nauyin mutane, don yă zama ba kai kaɗai ba ne mai ɗaukan kaya.


zan gangara in ga ko abin da suka yi ya yi muni kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”


Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”


Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ