Ayyukan Manzanni 5:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki9 Amma Bitrus ya ce mata, “Ƙaƙa kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, har sun iso bakin ƙofa ma, za su kuwa ɗauke ki, su fitar da ke.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
To, Elisha yana zaune a cikin gidansa, dattawa kuwa suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki ɗan aika yă ci gaba, amma kafin ɗan aikan yă isa, Elisha ya ce wa dattawan, “Kun gani ko? Wannan mai kisa ya aiko a cire mini kai! To, idan ɗan aikan ya iso, sai ku rufe ƙofar da ƙarfi, ku bar shi a waje. Ba da jimawa ba, maigidansa zai bi bayansa?”