14 Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen.
14 Da ya same mu a Asus, muka ɗauke shi a jirgin, muka zo Mitilini.
Mu kuwa muka ci gaba zuwa jirgin ruwan muka tashi muka nufi Assos inda za mu ɗauki Bulus. Ya yi wannan shirin don zai tafi can da ƙafa.
Kashegari muka tashi cikin jirgin ruwa daga can muka zo gefen Kiyos. Kwana ɗaya bayan wannan, sai muka ƙetare zuwa Samos, kashegari kuma muka iso Miletus.