20 Sa’ad da suka roƙe shi ya ƙara ’yan kwanaki da su, bai yarda ba.
20 Sai suka roƙe shi ya ƙara jimawa a wurinsu, amma bai yarda ba.
Batun ɗan’uwanmu Afollos kuwa, na roƙe shi sosai yă zo wurinku tare da ’yan’uwa. Bai so zuwa yanzu ba, amma zai zo in ya sami zarafi.
Bulus ya yanke shawara yă wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yă ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri yă kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentekos.
Suka isa Afisa, inda Bulus ya bar Firiskila da Akwila. Shi kansa ya shiga majami’a ya kuma yi muhawwara da Yahudawa.
Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Sa’an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.