Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 15:5 - Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

5 Amma waɗansu masu ba da gaskiya, 'yan ɗariƙar Farisiyawa, suka miƙe, suka ce, “Wajibi ne a yi musu kaciya, a kuma umarce su, su bi Shari'ar Musa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 15:5
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.”


Da suka ji haka, sai suka yabi Allah. Sa’an nan suka ce wa Bulus, “Ka gani ɗan’uwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka.


Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce.


“Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa


Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?


Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi.


Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa,


Amma muna so mu ji ra’ayinka, gama mun san cewa mutane ko’ina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.”


In an riga an yi wa mutum kaciya sa’ad da aka kira shi, to, kada yă zama marar kaciya. In an kira mutum sa’ad da yake marar kaciya, to, kada a yi masa kaciya.


Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake.


Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ