Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 15:36 - Sabon Rai Don Kowa 2020

36 Bayan ’yan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci ’yan’uwa a duk garuruwan da muka yi wa’azin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

36 An jima, Bulus ya ce wa Barnaba, “Bari yanzu mu koma mu dubo 'yan'uwa a kowane gari da muka sanar da Maganar Ubangiji, mu ga yadda suke.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 15:36
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye,


Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus.


Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum.


Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi.


Ina marmarin ganinku don in ba ku wata baiwar ruhaniya, don ku yi ƙarfi


A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata.


Sai Musa ya koma wurin Yetro surukinsa, ya ce masa, “Bari in koma wurin mutanena a Masar, in ga ko da mai rai a cikinsu.” Yetro ya ce, “Tafi, ka kuma sauka lafiya.”


Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki.


Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku.


Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok,


“Da Musa ya cika shekara arba’in da haihuwa, sai ya yanke shawara yă ziyarci ’yan’uwansa Isra’ilawa.


da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’


da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’


Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana ce wa makiyayan da suke lura da mutanena, “Domin kun watsar da garkena kuka kuma kore su ba ku kuma lura da su ba, zan kawo hukunci a kanku saboda muguntar da kuka yi,” in ji Ubangiji.


Kome ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara


Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.


Kowace rana Mordekai yana kai da komowa kusa da harabar filin gidan matan kulle, domin ya san yadda Esta take, da kuma abin da yake faruwa da ita.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ