Ayyukan Manzanni 13:17 - Sabon Rai Don Kowa 202017 Allahn mutanen Isra’ila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki17 Allahn jama'ar nan Isra'ila ya zaɓi kakanninmu, ya ɗaukaka jama'ar sa'ad da suke baƙunci a ƙasar Masar, da maɗaukakin iko kuma ya fito da su daga cikinta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?