Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 12:20 - Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

20 To, Hirudus ya yi fushi ƙwarai da mutanen Taya da na Sidon. Suka zo wurinsa da nufi ɗaya. Bayan sun rinjayi Bilastasa, sarkin fāda, suka nemi zaman lafiya, domin ga ƙasar sarkin nan suka dogara saboda abincinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 12:20
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai suka ba wa magina da kafintoci kuɗi, suka ba wa mutanen Sidon da na Taya abinci, da abin sha, da mai, don su kawo itatuwan al’ul a Yaffa daga Lebanon ta teku, yadda Sairus sarkin Farisa ya ba da umarni.


“ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.


“Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske.


In hankalin mai mulki ya tashi game da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.


kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya?


Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.


“Yanzu fa, bari ranka yă daɗe, yă aiko wa bayinsa alkama da sha’ir da kuma man zaitun da ruwan inabin da ka alkawarta,


Zan ba wa bayinka masu yankan katakai waɗanda suka yanka katako, garwa niƙaƙƙen alkama dubu ashirin, garwan sha’ir dubu ashirin da randunan ruwan inabi dubu ashirin da kuma randunan man zaitun dubu ashirin.”


Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib,


har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.


Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,


Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara; in kana yaƙi, ka sami bishewa.


A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi.


Bayan muka hangi Saifurus muka wuce shi ta kudu, sai muka ci gaba zuwa Suriya. Muka sauka a Taya, inda jirgin ruwanmu zai sauke kayansa.


Muka ci gaba da tafiyarmu daga Taya muka sauka a Tolemayis, inda muka gai da ’yan’uwa muka yi kwana ɗaya tare da su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ