Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.
Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika.
Yana cikin magana sai ga taro sun zo. Mutumin nan da ake kira Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun, shi ya bi da su. Sai ya matso kusa da Yesu don yă yi masa sumba.