26 Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu, kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi.
26 Haka kai ma za ka rayu, har ka tsufa da kyakkyawan tsufa.
Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa, za a kuwa ƙara wa ranka shekaru.
Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.”
Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa.
Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai, amma akan gajartar da shekarun mugaye.
Sa’an nan Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu da kyakkyawar tsufa, tsoho da kuma shekaru masu yawa; aka kuma tara shi ga mutanensa.
A ƙasarku, mace ba za tă yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.
“Mun yi nazarin wannan, kuma gaskiya ne. Saboda haka ka ji, ka kuma yi amfani da shi.”
“A cikinta ba za a ƙara jin jariri ya rayu na ’yan kwanaki kawai ba, ko kuwa wani tsohon da bai cika kwanakinsa ba; duk wanda ya mutu yana da shekaru ɗari za a ce ya mutu a kurciya ne kawai; duk wanda bai kai ɗari ba za a ɗauka la’antacce ne.
Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya mutu, duk da haka idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuwa bai ragu ba.