17 Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.
17 Sa'an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.
Sa’an nan Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu da kyakkyawar tsufa, tsoho da kuma shekaru masu yawa; aka kuma tara shi ga mutanensa.
Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa.
Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.”
Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu, kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi.
saboda ku, ’ya’yanku, da kuma ’ya’yansu bayansu za su ji tsoron Ubangiji Allahnku muddin kuna rayuwa ta wurin kiyaye dukan ƙa’idodinsa da umarnan da na ba ku, da kuma don ku yi tsawon rai.
Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu.