22 Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji, itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
22 Gama inuwar da take rufe ta ta ƙaddaji ce, Itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
“ ‘Ta ɗebi waɗansu irin ƙasarku ta sa a ƙasa mai taƙi. Ta shuka shi kamar itacen wardi kusa da ruwa mai yawa,
Saboda haka dukiyar da suka tara suka kuma ajiye sun ɗauka suka ƙetare Rafin Arabim da su.
A rana ta fari, za ku ɗebi zaɓaɓɓun ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, da rassan dabino, rassa masu ganye, da kuma ganyayen itacen wardi na rafi, ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, kwana bakwai.
Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus ta ɓuya cikin kyauro da fadama.
Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba; ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa.
Za su tsiro kamar ciyawa a wuriyar ruwa, kamar kurmi kusa da rafuffuka masu gudu.