18 In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi,
18 Allah ba ya amince wa barorinsa na cikin sammai, Yakan sami laifi a wurin mala'ikunsa.
Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan.
Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci;
Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa.
“Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?
Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?