Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe.
Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.
Sai ya ce, “Daniyel, kai ne wanda ake ƙauna sosai, ka yi lura da kyau game da kalmomin da zan yi maka magana a kansu, ka tashi yanzu, gama an aiko ni a gare ka.” Sa’ad da ya faɗa mini haka, sai na tashi a tsaye ina rawan jiki.
Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”