23 Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa.
23 Kibau na ta shillo a kansa, Māsu suna ta gilmawa a gabansa.
Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.
Yana kartar ƙasa da ƙarfi; ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho.
Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro.