Annabci, maganar Ubangiji game da Isra’ila. Ubangiji, wanda ya shimfiɗa sammai, wanda ya kafa harsashin duniya, wanda kuma ya yi ruhun mutum a cikinsa ya ce,
Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, na kafa dutse a Sihiyona, dutsen da aka gwada, dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe; wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.
Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka; Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi. An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.
Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su, ’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai da sassaƙa don adon fada.
Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka; yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki; yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka. “Harsashin duniya na Ubangiji ne; a bisansu ne ya kafa duniya.