Suna guje wa Isra’ilawa suna gangarawa a kan hanyar Bet-Horon har zuwa Azeka, sai Ubangiji ya turo manyan duwatsu daga sararin sama suka karkashe su, waɗanda manyan duwatsun suka kashe sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi.
Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa, gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara.
Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai.
ƙanƙara ta fāɗo, walƙiya kuma tana ta wulƙawa. Wannan ce ƙanƙara mafi munin da aka taɓa yi, a dukan ƙasar Masar, tun tarihin kahuwarta na zaman al’umma.