Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa.
Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku kafin ya kawo duhu, kafin ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan tuddai masu duhu. Za ku sa zuciya ganin haske amma zai mai da shi duhu mai kauri ya kuma canja shi zuwa duhu baƙi ƙirin.
Yayinda abokan gāba suka gangaro wajensa, sai Elisha ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ka sa mutanen nan su zama makafi.” Sai Ubangiji ya buge su da makanta kamar yadda Elisha ya roƙa.