Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.
Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa, “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki, ya Ubangiji Maɗaukaki. Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya, ya Sarkin zamanai.
Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba.
“Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka.
Shi Dutse ne, ayyukansa cikakku ne, dukan hanyoyinsa kuwa masu adalci ne. Allah mai aminci, wanda ba ya yin rashi gaskiya, shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.
Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji, sa’ad da na kawo ƙara a gabanka. Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka. Me ya sa mugaye suke nasara? Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa?