14 In nufinsa ne ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa,
14 Da zai amshe ruhu da numfashin da ya hura wa mutum,
Sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai su razana; sa’ad da ka ɗauke numfashinsu, sai su mutu su kuma koma ga ƙura.
Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?
Za a tattara su tare kamar ɗaurarru a kurkuku; za a rufe su a kurkuku a kuma hukunta su bayan kwanaki masu yawa.
“Mene ne mutum har da ka kula da shi haka, har ka mai da hankali a kansa,
Ran kowace halitta yana a hannunsa, haka kuma numfashin dukan ’yan adam.
Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku ’ya’yan mutane.”
turɓaya ta koma ƙasar da ta fito, rai kuma yă koma ga Allah wanda ya ba da shi.