Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.
manufofinka da girma suke, ayyukanka kuma masu girma ne. Idanunka suna a buɗe ga dukan hanyoyin mutane; kakan sāka wa kowa gwargwadon halinsa yadda ya dace.
Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma.
In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba?
Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa. Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa.