Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.
Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.
Kada ka bar bakinka ya kai ga yin zunubi. Kada kuma ka kai ƙara wurin ɗan saƙon haikali cewa, “Alkawarin da na yi kuskure ne.” Me ya sa Allah yake fushi a kan abin da ka faɗa har yă lalatar da aikin hannuwanka?
Kada ka yi subul da bakinka, kada zuciyarka tă yi garajen furta wani abu a gaban Allah. Allah yana sama kai kuma kana duniya, saboda haka, kada kalmominka su zama da yawa.