Ba wanda yake da iko a kan iska har da zai riƙe ta, saboda haka babu mai iko kan ranar mutuwarsa. Kamar yadda ba a sallamar mutum a lokacin yaƙi, haka ma mugunta ba za tă saki masu aikata ta ba.
Kamar ruwan da ya zuba a ƙasa, wanda ba a iya kwasa, haka dole mu mutu. Amma Allah ba ya ɗaukan rai; a maimako, yakan ƙirƙiro hanyoyi domin mutumin da aka kora kada yă kasance yasasshe daga gare shi.
“Yanzu na kusa barin fuskar duniyan nan. Kun sani da dukan zuciyarku, da dukan ranku cewa, Ba ko ɗaya daga cikin alkawuran da Ubangiji Allahnku ya yi, da bai cika ba. Kowane alkawari ya cika; ba ko ɗaya da bai cika ba.