2 Ina amfani ƙarfin hannuwansu gare ni, tun da ba su da sauran kuzari?
2 Wace riba zan samu ta wurin ƙarfin hannuwansu waɗanda ba su da sauran kuzari?
“Amma yanzu suna yi mini ba’a waɗanda na girme su, waɗanda iyayensu maza ba su isa su zama karnukan kiwon garken tumakina ba.
Duk sun rame don rashi da yunwa, suna yawo a gaigayar ƙasa a kufai da dare.
Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka, kafin lokacin wahala ta zo shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu,”