Ba sun kwanta tare da sauran jarumawa marasa kaciyan da aka kashe, waɗanda suka gangara kabari tare da makaman yaƙinsu, waɗanda aka yi musu matashin kai da takubansu ba? Hukuncin zunubansu yana a bisa ƙasusuwansu, ko da yake tsoron waɗannan jarumawa ya manne cikin ƙasar masu rai.