“Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub, dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila, ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku, na kuma riƙe ku tun haihuwarku.
Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni, mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi! Ban ba da bashi ko in ci bashi ba, duk da haka kowa yana zagina.
Mutum zai iya kasance da ’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa.