Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin, “Allah yana gāba da mai girman kai, amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”
Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.