Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi.
Na ce, “Ba zan ƙara ganin Ubangiji ba, Ubangiji a ƙasa ta masu rai; ba zan ƙara ga wani mutum, ko in kasance tare da waɗanda suke zama a wannan duniya ba.
Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”
“Elam tana can, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu sun mutu, an kashe su da takobi. Dukan waɗanda suka haddasa tsoro a ƙasar masu rai sun gangara wurin marasa kaciya a duniyar da take ƙarƙashi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.