Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.
Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta; zan tace su kamar azurfa in gwada su kamar zinariya. Za su kira bisa sunana zan kuwa amsa musu; zan ce, ‘Su mutanena ne,’ za su kuma ce, ‘Ubangiji ne Allahnmu.’ ”
Dukan kwaf Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon, zinariya ce zalla. Babu wani abin da aka yi da azurfa, domin ba a ɗauki azurfa a bakin kome ba a zamanin Solomon.
Sa’ad da raƙuman suka gama shan ruwa, mutumin ya fitar da zoben hanci na zinariya mai nauyin giram biyar da woroworo biyu na zinariya masu nauyin shekel goma, ya ba ta.