Ko da yake suna azumi, ba zan saurari kukansu ba, ko da yake suna miƙa hadayun ƙonawa da hadayun gari, ba zan yarda da su ba. A maimako zan hallaka su da takobi, yunwa da annoba.”
Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini!
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan kawo masifa a kansu wadda ba za su iya tsere mata ba. Ko da yake suna kuka gare ni, ba zan saurare su ba.
Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’ “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’