Duk masu wucewa suna yi miki tafi na reni; suna yi wa Diyar Urushalima tsaki suna kaɗa kai suna cewa, “Wannan ne birnin da aka ce kyakkyawa ne, mai farantawa dukan duniya rai?”
Birnin da yake harka ke nan da take zaune lafiya. Ta ce wa kanta, “Ni ce, kuma babu kamata.” Dubi irin kangon da ta zama mana, mazaunin namun jeji! Duk wanda ya wuce ta sai ya yi mata tsaki yana kaɗa kai.
Wannan haikali zai zama tarin juji. Duk wanda ya wuce ta hanyan nan kuwa zai ji tausayi, yă kuma yi tsaki yana cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka ga wannan ƙasa da kuma wannan haikali?’
Kuna kiyaye ƙa’idodin Omri da dukan ayyukan gidan Ahab kun kuma bi al’adunsu. Saboda haka, zan maishe ku kufai in mai da ku abin dariya a cikin mutane, za ku sha reni a wurin al’ummai.”
Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun tafa hannuwanku kuka kuma buga ƙafafunku, kuna farin ciki don nuna dukan ƙiyayyarku a kan ƙasar Isra’ila,
Ba abin da zai warkar da rauninka; rauninka ya yi muni. Duk wanda ya ji labarinka zai tafa hannuwansa saboda farin cikin fāɗuwarka, gama wane ne bai ji jiki a hannunka ba?