Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,
In fa kuka yi alkawari ga Ubangiji Allahnku, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama tabbatacce Ubangiji Allahnku zai neme shi daga gare ku, za ku kuma zama masu laifin zunubi.
Yabez ya yi kuka ga Allah na Isra’ila ya ce, “Ka yi mini albarka ka fadada yankina! Bari hannunka yă kasance tare da ni, yă kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni, don kada in shiga wahala.” Sai Allah ya ji roƙonsa.
Da ya yi addu’a gare shi, sai Ubangiji ya taɓu da tubansa, ya kuma saurari roƙonsa; saboda haka ya dawo da shi Urushalima da kuma zuwa mulkinsa. Sa’an nan Manasse ya san cewa Ubangiji shi ne Allah.