Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 21:19 - Sabon Rai Don Kowa 2020

19 An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’ Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

19 “Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa. A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi. Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 21:19
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina,


“Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa, “ ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’?


“A waɗannan kwanaki mutane ba za su ƙara ce, “ ‘Ubanni suka ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya suka mutu ba.’


A shirya wuri don a yayyanka ’ya’yansa maza saboda zunuban kakanninsu; kada a reno su su gāji ƙasar su cika duniya da biranensu.


Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku; ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi. Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata.


Alekzanda maƙerin ƙarafan nan ya yi mini mugunta ƙwarai. Ubangiji zai sāka masa saboda abin da ya yi.


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci.


“Amma a ce wannan ɗa yana da ɗa wanda ya ga dukan zunuban da mahaifinsa yake aikata, kuma ko da yake ya gan su, bai yi ko ɗaya daga cikin irin abubuwan nan ba, wato,


Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su.


“Ban jibge wannan a ma’ajiya na kuma yimƙe shi a taskokina ba?


Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.


Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.


Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,


A yau, ko da yake ni naɗaɗɗen sarki ne, duk da haka na raunana, kuma waɗannan ’ya’yan Zeruhiya sun fi ƙarfina. Ubangiji yă sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata!”


sa’ad da na wasa takobi mai walƙiya hannuna kuwa ya cafke shi don yin hukunci, zan ɗau fansa a kan abokan gābana in sāka wa waɗanda suke ƙina.


Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.”


‘Ubangiji mai jinkiri fushi ne, mai yawan ƙauna, mai gafarta zunubi da tawaye. Duk da haka ba ya ƙyale mai laifi, babu horo. Yana horin ’ya’ya saboda zunubin iyayensu har tsara ta uku, da ta huɗu.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ