2 “Tunanin da ya dame ni ya sa dole in amsa domin abin ya dame ni sosai.
2 “Ayuba, ka ɓata mini rai, Ba zan yi haƙuri ba, sai na ba ka amsa.
Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.
Cikin tsorona na ce, “An yanke ni daga gabanka!” Duk da haka ka ji kukata na neman jinƙai sa’ad da na kira gare ka don taimako.
’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,
Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba.
Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan.”
Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba ba zan ƙara yin magana da sunansa ba,” sai in ji maganarsa a cikina kamar wuta, wutar da aka kulle a ƙasusuwana. Na gaji da danne ta a cikina; tabbatacce ba zan iya ba.
Kada ranka yă yi saurin tashi, gama fushi yana zama a cinyar wawaye.
Ka ga mutum mai yin magana da garaje? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.”
Na ji wani zargin da ka yi mini na reni, kuma yadda na gane, shi ya sa zan ba da amsa.
Ko wani zai ce ga laifin da na yi? In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu.
“In wani ya yi maka magana, za ka ji haushi? Amma wa zai iya yin shiru?
Sai Zofar mutumin Na’ama ya amsa,