Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 2:11 - Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

11 Sa'ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na'ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta'azantar da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 2:11
34 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.


Dukan ’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya.


Game da Edom. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Babu sauran hikima a Teman ne? Shawara ta ɓace daga masu basira ne? Hikimarsu ta ruɓe ne?


Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.


“Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.


In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.


Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.


Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu.


“Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina.


“Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan; dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!


Ayarin Tema sun nemi ruwa, matafiya ’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu.


’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. ’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan.


Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi.


Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa, ’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz,


’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.


Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.


Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki, wa zai ta’azantar da ke? Lalaci da hallaka, yunwa da takobi, wa zai ƙarfafa ki?


Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.


Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.


Bayan Ubangiji ya gaya wa Ayuba waɗannan abubuwa, ya ce wa Elifaz mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokanka guda biyu domin ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.


Duk abokaina sun yashe ni; waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.


Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne yayinda nake kuka ga Allah;


Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku!


Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.


Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya.


Saboda haka Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa da Zofar mutumin Na’ama, suka yi abin da Ubangiji ya gaya masu; Ubangiji kuma ya karɓi addu’ar Ayuba.


Jarumawanki, ya Teman, za su razana, za a kashe kowane mutum a duwatsun Isuwa.


Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.


Gederot, Bet-Dagon, Na’ama, Makkeda, garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.


Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ