Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
“Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.” Bari yă zama haka nan! Amin.
Yanzu kam muna ganin abubuwa kamar a madubi sai dai ba sosai ba, amma a ranan nan za mu gani fuska da fuska. Yanzu kam sanina ba cikakke ba ne, amma a ranan nan zan kasance da cikakken sani, kamar dai yadda Allah ya san ni a yanzu.
shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.