“Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu, ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul kuma mai ƙarfi kamar itacen oak. Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama, da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.
Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe kara kuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta, haka saiwarsu za su ruɓa iska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura; gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukaki suka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila.