1 Na karaya, kwanakina sun kusa ƙarewa, kabari yana jirana.
1 “Ƙarshen raina ya gabato, da ƙyar nake numfashi, Ba abin da ya rage mini sai kabari.
Ba zan tuhume su har abada ba, ba kuwa kullum zai yi fushi ba, gama a haka ruhun mutumin zan yi suma a gabana, shi numfashin mutumin da na halitta.
Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu.
Numfashina yana ɓata wa matata rai; ’yan’uwana sun ƙi ni.
“Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya? Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri?
“Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri, za su kawo ga ƙarshe ba bege.
“Shekaru kaɗan suka rage in kama hanyar da ba a komawa.
Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci haka kuma abubuwan da zuciyata take so.