5 In da za ku yi shiru gaba ɗaya! Zai zama muku hikima.
5 Kada ku faɗi kome, Wani sai ya ce kuna da hikima!
Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.
“Ku yi shiru zan yi magana; sa’an nan abin da zai same ni yă same ni.
’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,
Kamar yadda son cika buri yakan zo sa’ad da kana da yawan damuwa, haka jawabin wawa yake sa’ad da yake yawan magana.
Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka, gama lokutan mugaye ne.
Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne.
“Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba ku kuma murƙushe ni da maganganunku?
“Yaushe za ka gama maganganun nan? Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.
Dogayen surutanku ba sa ƙare ne? Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?
Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru? Ba wanda zai kwaɓe ka lokacin da kake faɗar maganar da ba daidai ba?
Ku ji gardamata yanzu; ku ji roƙon da zai fito daga bakina.
Ku dube ni, ku kuma yi mamaki; ku rufe bakina da hannunku.
Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru, yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa.