13 “Ku yi shiru zan yi magana; sa’an nan abin da zai same ni yă same ni.
13 “Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana. Duk abin da zai faru, ya faru.
“Saboda haka ba zan yi shiru ba; zan yi magana cikin ɓacin raina, zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina.
Ku ba ni zarafi in yi magana, bayan na gama sai ku yi ba’arku.
In da za ku yi shiru gaba ɗaya! Zai zama muku hikima.
“Na gaji da rayuwa; saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi yadda raina yake jin ba daɗi.
Duk surutanku kamar toka suke; kāriyarku na yimɓu ne.