Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.” Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora.
Kamar makafi, sai lallubar bango muke yi, muna lallubawar hanyarmu kamar marasa idanu. Da tsakar rana muna tuntuɓe sai ka ce wuri ya fara duhu; cikin ƙarfafa, mun zama kamar matattu.
Da tsakar rana za ku riƙa lallubawa kamar makaho. Za ku zama marasa nasara a cikin kome da kuka yi; kowace rana za a zalunce ku, a kuma yi muku ƙwace, ba tare da wani ya cece ku ba.