20 Yana sa amintattun mashawarta su yi shiru yakan kawar da hikimar dattawa.
20 Yakan rufe bakin waɗanda aka amince da su. Yakan kawar da hikimar tsofaffi.
Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba, ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba.
Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba, saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.
Yana hana shugabannin duniya ganewa; Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata.
Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada, amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.
Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.
Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta.