A wannan lokaci zan bincike Urushalima da fitilu in kuma hukunta waɗanda ba su kula ba, waɗanda suke kamar ruwan inabin da aka bar a ƙasan tukunya, waɗanda suke tsammani, ‘Ubangiji ba zai yi kome ba nagari ko mummuna.’
Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.